Van Gaal bai ji dadin jadawalin wasa ba

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Van Gaal ya ce wasannin da za su buga za su hana shi ganin iyalansa lokacin Kirsimeti

Kocin Manchester United Louis Van Gaal ya nuna rashin jin dadi da yadda aka sanya wa klob din wasanni a lokacin bukukuwa.

Klob din United zai buga wasanni hudu a cikin kwanaki 9 daga washegarin Kirsimeti zuwa ranar 3 ga watan Janairu, dai dai da jadawalin gasar kofin kalubale.

United za ta kara da Newcastle a washe garin Kirsimeti a gasar Premier, sannan kuma ta hadu da Tottenham bayan kwanaki biyu, kafin kuma ta fafata da Stoke City a ranar sabuwar shekara.

Van Gaal mai shekaru 63 ya ce "ina da mata da yara da kuma jikoki, ba zan samu ganinsu ba kenan a lokacin Kirsimeti".

Sai dai Kocin ya ce dole haka zai rungumi tsarin saboda ya na so ya taka rawar gani a gasar ta Premier.