Manchester United ta doke Stoke da ci 2-1

Manchester United Stoke City Hakkin mallakar hoto pa
Image caption United tana matsayinta na hudu a teburin Premier

Manchester United ta doke Stoke City da ci 2-1, a gasar Premier wasan mako na 14 da suka kara a Old Trafford ranar Talata.

United ce ta fara zura kwallon farko ta hannun Marouane Fellaini, yayin da Stoke City ta farke kwallo ta hannun Steven N'Zonzi.

Juan Mata ne ya kara zura kwallo ta biyu a bugun tazara, kuma hakan ya sa ta ci gaba da zama a matsayinta na hudu a teburin Premier.

Ga sauran sakamakon wasannin da aka kara:

Burnley 1 - 1 Newcastle Leicester 1 - 3 Liverpool Swansea 2 - 0 QPR Crystal Palace 0 - 1 Aston Villa West Brom 1 - 2 West Ham