Za a fara amfani da na'ura a Bundesliga

Goal Line Technology Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A gasar badi Jamus za ta fara amfani da na'urar a raga

Kungiyoyin kwallon kafa na Bundesliga ta Jamus sun amince da fara amfani da na'urar fasahar tantance shigar kwallo raga daga kakar wasanni ta badi.

Kulob din Bayern Munich ne ya kawo shawarar fara amfani da na'urar, a inda kungiyoyi 15 suka kada kuri'ar amincewa da hakan.

Mahukuntan gasar Bundesligar sun amince da yin amfani da na'urar ne domin yanke takaddamar shigar kwallo cikin raga a sauwake.

Tun a shekarar bara aka fara amfani da fasahar a gasar Premier, aka kuma yi amfani da ita a gasar cin kofin duniya da aka kammala a Brazil.