Adidas ya ki tsawaita kwantiragi da Nigeria

Ahmed Uche. Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria ba za ta kare kambunta a Equitorial Guinea ba

Kamfanin Adidas na Jamus mai sama wa tawagar Super Eagles kayayyakin wasan tamaula ya ki ya sabunta kwantiraginsa da Nigeria.

Adidas ya yi korafi a watan Agusta cewar masu horas wa da 'yan wasan tawagar Super Eagles sun karya yarjejeniya, a inda suka dinga saka kayayyakin wasu kamfanoni.

Hakan ya sa Nigeria ta yi rashin dalar Amurka miliyan bakwai da Adidas ke bai wa kasar a kowacce shekara domin saka kayan da yake yi.

Hukumar kwallon kafa ta Nageriya ta ce tana shan wahala matuka wajen nemo kamfanin da zai maye gurbin Adidas.

Nigeriya ta yi fama da matsaloli a harkar wasan kwallon kafa, na baya-bayan nan shi ne kasa samun tikitin shiga gasar cin kofin Afirka domin kare kambunta.