Aston Villa ta doke Leicester da ci 2-1

Aston Villa Leicester Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Villa ta koma mataki na 11 a teburin Premier bayan buga wasanni 15

Aston Villa ta hada maki uku bayan da ta doke Leicester da ci 2-1 a gasar Premier wasan mako na 15 da suka kara a Villa Park ranar Lahadi.

Leicester ce ta fara zura wa Villa kwallo a raga ta hannun Ulloa a minti na 13 da fara kwallo, kafin minti hudu tsakani Villa ta farke kwallonta ta hannun Clark.

Leicester ta karasa wasan ne da 'yan kwallo 10, bayan da aka bai wa Konchesky jan kati, kuma karo na tara kenan ana korarsa a wasa tun lokacin da ya zama kwararren dan kwallo.

Aston Villa ta zura kwallonta na biyu ta hannun Hutton a minti na 71, wanda hakan ne ya sa ta hada maki uku a karawar.

Nasarar da Villa ta samu ya sa ta koma matsayi na 11 a teburin Premier da maki 19, yayin da Leicester ke ci gaba da zama ta karshe a teburin da maki 10 kacal.