Ba za mu dogara da Gerrard ba — Rodgers

Steven Gerrard Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool za ta ziyarci Manchester United ranar Asabar

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya umarci 'yan wasansa da su kara kaimi su kuma rage dogaro da Steven Gerrard ko da baya cikin wasa.

Gerrard, mai shekaru 34, ba a fara wasan da suka tashi babu ci da Sunderland da shi ba, a gasar Premier da suka buga, kuma karo na biyu kenan ba a fara wasa da shi a gida.

Sai a minti na 67 ne koci Rodgers ya saka Gerrard a wasa, kuma duk da saka shin suka tashi wasa babu ci a karawar da suka yi a Anfield.

Gerrard ba ya cikin 'yan wasan farko da za su kara da Basel a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Talata, kafin Liverpool din ta ziyarci Manchester United a wasan Premier ranar Asabar.