Ronaldo ya kafa tarihin zura kwallaye a La Liga

Real Madrid Team
Image caption Real Madrid ce ke matsayi na daya a teburin La Liga

Cristiano Ronaldo ya jagoranci Real Madrid lashe wasanni 18 a jere da ta buga a dukkan karawa da ta yi a bana, bayan da ta doke Celta De Vigo 3-0 ranar Asabar.

Ronaldo ne ya zura dukkan kwallaye uku a ragar Celta De Vigo a karawar da suka yi a Bernabeau, kuma karo na 23 kenan yana cin kwallaye uku a wasa.

Dan wasan, mai shekaru 29, ya kuma zura kwallaye 200 a gasar La Liga daga cikin wasanni 178 da ya buga wa Real Madrid tamaula.

Ronaldo wanda ake hasashen shi ne zai lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar bana, ya doke tarihin da Alfredo Di Stefano da Telmo Zarra suka kafa na yawan zura kwallaye uku a wasa.

Haka kuma Madrid ta yi kankankan da tarihin da Barcelona ta kafa na yawan lashe wasanni 18 a dukkan karawar da Frank Rijkaard ya jagoranci kulob din daga tsakanin Oktoban 2005 zuwa Janairun 2006.