Kila Aguero ba zai buga wasa da Roma ba

Sergio Aguerro Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester City na bukatar doke Roma a Italiya

Watakila Sergio Aguero ba zai buga wa Manchester City karawar da za tayi da Roma wasan gasar cin kofin zakarun Turai, sakamakon raunin da ya ji.

Dan kwallon Argentina, mai shekaru 26, ya ji raunin ne a karawar da suka yi da Everton, lokacin da Muhamed Besic ya yi masa keta a karawar da suka yi ranar Asabar.

Ranar Laraba ne City za ta ziyarci Roma a gasar cin kofin zakarun Turai, kuma tana bukatar doke Roma domin ta kai wasan zagayen gaba.

Aguero, shi ne ke kan gaba wajen zura kwallaye a raga a gasar Premier, inda ya zura kwallaye 14 a bana, kuma ba a bayyana tsawon lokacin da zai yi jinya ba.