CAF na takaicin rashin Nigeria a kofin Afirka

Issa Hayatou Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria ba ta kare kambunta a shekarar 1996 a Afirka ta Kudu ba

Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Afirka, Issa Hayatou, ya ce ya ji takaici da Nigeria ba za ta kare kambunta a Gasar cin Kofin Nahiyar Afirka na badi ba.

Ya kuma kara da cewar kasa samun tikitin shiga gasar da kasar ta kasa yi ba zai dasashe mahimmancin ta a harkar kwallon Afirka ba.

Nigeria ta kasa samun tikitin shiga gasar a badi ne domin kare kambunta a Equitorial Guinea, inda ta kare a matsayi na uku a rukunin farko na wasan neman tikitin da maki takwas.

Maki takwas da ta samu a rukunin kuma ya kasa saka ta a cikin 'yan alfarma domin fafatawa a gasar da za a fara daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairun badi.

Hayatou ya sanarwa da shugaban Hukumar Kwallon Kafar Nigeria Amanju Pinnick cewa masoya kwallon kafa a Afirka za su yi takaicin rashin Super Eagles a gasar, wadda ita ce mafi girma a Afirka.