Manchester United ta koma ta 3 a teburin Premier

Robin van Persie Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption United ta koma matsayi na uku a teburin Premier

Kungiyar Manchestere United ta koma matsayi na uku a teburin Premier, bayan da ta doke Southampton da ci 2-1 a gasar Premier wasan mako na 15.

United ce ta fara zura kwallo ta hannun Robin van Persie a minti na 12 da fara tamaula, yayin da Graziano Pelle ya farke wa Southampton kwallo a minti na 31.

Southampton ta barar da damar zura kwallo da yawa, sai dai van Persie ne ya tabbatarwa da United maki uku a wasan, a inda ya zura kwallo ta biyu a minti na 71.

Nasarar da United ta samu ta sa ta koma mataki na uku a teburin Premir da maki 28, ita kuwa Southampton ta koma matsayi na biyar da maki 26.

Ranar Lahadi Manchester United za ta karbi bakuncin Liverpool a wasan mako na 16.