Magoya bayan Real Madrid sun zagi Messi

Hakkin mallakar hoto ALLSPORT
Image caption An ce an gano wasu daga cikin masu zagin

Za a kai karar magoya bayan Real Madrid da suka zagi Lionel Messi da Barcelona zuwa hukumar kwallon Spain (RFEF).

Shugaban gasar La Liga Javier Tebas ya ce ba za a lamunci zagin da aka yi a Bernabue ba.

Magoya bayan Real sun yi kalaman batanci ga kungiyar da ke hammaya da su Barcelona, sannan kuma suka zagi Messi a wasansu da Celta Vigo a ranar asabar.

Kafofin yada labarai a Spain sun ce an gano magoya bayan Real 17 kuma an ladabtar da su.

Tebbas ya ce "mun dauki mataki kuma za mu ci gaba bin wannan tafarkin."