Oliseh yana fargaba kan makomar kwallon Nigeria

Sunday Oliseh Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sunday Oliseh tsohon dan wasan Super Eagles

Tsohon dan kwallon Nigeria, Sunday Oliseh, ya ce martabar Super Eagles ba za ta dawo ba har sai an yi gyare-gyaren da ya kamata a yi.

Nigeria ta rasa tagomashinta a harkar tamaula, inda ko da a bayan nan ta kasa samun tikitin shiga gasar cin kofin Afirka da domin kare kambunta a Equitorial Guinea a badi.

Oliseh ya shaida wa BBC cewar, "Nigeria tana da matsala a fannin tsare-tsare da kuma gudanarwa, kuma matsala ce mai girma ga kasa".

Dan wasan ya san matsalolin Nigeria domin yana cikin tawagar 'yan kwallon da suka dauko wa kasar kofin Afirka a shekarar 1994, da lambar zinare a gasar Olympic a shekarar 1996.

Oliseh ya buga wa Nigeria gasar cin kofin duniya a shekarar 1994 da 1998, wanda ya taimaka mata kai wa wasan kasashe 16 da suka rage a gasar.