'Yan sanda na tuhumar shugaban Bastia

Pierre-Marie Geronimi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kulob din ya tabbatar da cewa 'yan sanda sun gayyaci shugaban

'Yan sandan Faransa sun kama shugaban kulob din Bastia, Pierre-Marie Geronimi, wanda suke bincika kan almubazzaranci da kudin kulob din.

Ana binciken shugaban ne dangane da aikin shinfida ciyawar roba da aka yi a filin wasan matasan kulob din, da kuma biyan kudade ga abokan hulda har da wani kamfanin sufuri.

Kungiyar kwallon kafa ta Bastia tana matsayi na karshe a teburin gasar Faransa wato Ligue 1.

Sai dai mahukuntan Bastia, sun karyata yin almubazzaranci da kudin kulob din, inda suka ce kudin da aka biya wani kamfanin sufurin ladan jigilar 'yan wasa ne da ya yi zuwa filin atisaye.