Sankhare zai buga wa Senegal kwallo

Younousse Sankhare Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a fara tsakanin 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairun badi

Tsohon matashin dan kwallon Faransa, Younousse Sankhare, ya ce zai buga wa Senegal tamaula idan har kasar ta gayyace shi.

Dan wasan, mai shekaru 25, wanda ke murza leda a kulob din Guingamp ta Faransa, zai iya buga wa Teranaga Lions kwallo, domin kasar mahaifansa ce.

A dokar hukumar kwallon kafa ta FIFA, Sankhare zai iya buga wa Senegal tamaula, tun da bai buga wa babbar tawagar kwallon kafar Faransa wasa ba.

Senegal za ta iya gayyato Younousse Sankhare ya buga mata gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a fara a Equitorial Guinea a badi.