Mun samu sa'a a kan Southampton - Van Gaal

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Van Gaal ya ce ba su taka leda sosai ba, sa'a akwai suka yi a kan Southampton

Kocin Manchester United Louis van Gaal ya ce sa'a kawai suka samu a wasan da suka doke Southampton da ci 2-1.

Kwallaye biyu da Robin van Persie ya zura sun bai wa United nasarar zama ta uku a saman tebirin gasar Premier.

Van Gaal ya shaida wa BBC cewa, "Idan 'yan wasanka suna da kyau, to lallai ka cancanci yin nasara a duk wasan da ka yi. Wasan da muka taka ba shi da kyau sosai, mun dai taki sa'a".

Ya yabawa Van Persie bisa rawar da ya taka a wasan da suka yi a Southampton.