An yi barazanar kashe Faustino Asprilla

Faustino Asprilla Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya ce ya firgita da barazanar da aka yi masa

Wasu 'yan bindiga sun yi wa tsohon dan kwallon Newcastle, Faustino Asprilla, barazanar za su kashe shi, wanda hakan ya sa ya bar gidansa na Colombia.

'Yan bindigar da suka boye fuskokinsu, sun shiga gidan da yake a Tulua, inda suka bukaci ya ba su kudi, kuma ya tuntubi shugabansu in ba haka ba za su kashe shi da iyalansa.

Aspirilla wanda ya buga wa Newcastle wasa sau 54 tsakanin 1996 zuwa 1998, ya ce ya bar gidan da yake ne domin ya tsira da rayuwarsa da ta iyalansa.

Lokacin da yake buga wa Newcastle tamaula ya zura kwallaye 12, ciki har da kwallaye uku da ya ci Barcelona a wasan da suka tashi 3-2 a gasar zakarun Turai a shekarar 1997.