Mali ce za ta lashe kofin Afirka — Yatabare

Sambou Yatabare Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tawagar kwallon kafar Mali na fatan lashe kofin Afirka a badi

Dan kwallon Mali mai wasan tsakiya Sambou Yatabare ya ce kasarsa za ta iya lashe kofin nahiyar Afirka da za a fara a watan Janairun badi.

Mali wacce ba ta taba daukar kofin ba, ta samu kai wa matsayi na biyu a shekarar 1972, ta kuma taba zama ta uku a shekarun 2012 da 2013.

Yatabare, mai shekaru 25, ya shaida wa BBC cewar "Tawagar 'yan wasan Mali suna da kwarin gwiwa, kuma idan za su buga wasan da ya da ce lallai za su iya lashe kofin gasar".

Congo ce ta doke Mali da ci 3-2 a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Kamaru ta karbi bakunci shekaru 42 da suka gabata, kuma 'yan wasanta na yanzu na hankoron lashe kofin da za a fafata a Equitorial Guinea.