Tottenham ta bai wa Adebayor hutu

Emmanuel Adebayor Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kwallaye biyu kacal dan wasan ya zura a kakar wasan bana a Tottenham

Kulob din Tottenham ya bai wa dan wasansa mai buga gaba Emmanuel Adebayor, hutu domin ya ziyarci Togo bisa dalilai na kashin kai.

Wannan na nufin dan wasan, mai shekaru 30, ba zai buga karawar da kulob din zai yi da Besiktas a gasar Europa League, kuma dama yana yin jinya ne.

Tottenham ba ta yi karin bayani dangane da bai wa dan wasan hutu ba, sai dai ta fada a shafinta na twitter cewar batun sirri ne.

Tsohon dan kwallon Arsenal ya buga wa Tottenham wasanni 12 a kakar wasanni ta bana, inda ya zura kwallaye biyu a raga.

Rabon da Adebayor ya buga wa Tottenham kwallo tun cikin watan Nuwamba, lokacin da Togo ta kasa samun tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka na badi.