'Liverpool tana ci gaban mai hakan rijiya'

Liverpool FC Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool tana matsayi na tara a teburin Premier

Kulub din Liverpool yana ci gaba da yin baya a wasanninsa duk da nasarar da ya samu a bara in ji tsohon dan wasan kulob din Mark Lawrenson.

Lawrenson ya damu, har ma ya soki Brendan Rodgers da ci gaba da sauya 'yan wasa kamar yadda yake canja safunan sawarsa a duk wasan da Liverpool za ta yi.

Haka kuma ya ce an dogara kocokan cewar Daniel Sturridge shi ne zai iya ceto kulob din daga halin da ya tsinci kansa.

An cire Liverpool a gasar cin kofin zakarun Turai na bana, kuma tana matsayi na tara a teburin Premier.

Liverpool za ta ziyarci Manchester United a karawar da za suyi a gasar Premier wasan mako na 16 a Old Trafford.