Anceloti ya bukaci Madrid ta lashe wasa na 20 a jere

Carlo Ancelotti Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Real Madrid ce ta daya akan teburin La Ligar Spaniya

Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya umarci 'yan kwallonsa da su ci gaba da tsawaita lashe wasa ba tara da an doke su ba, a shirin karawar da za suyi ranar Juma'a.

Madrid wacce za ta kara da Almeria a gasar La Liga, ta kafa tarihin lashe wasanni 19 a jere, bayan da ta doke Ludogorets a gasar cin kofin zakarun Turan ranar Talata.

Kulob din Barcelona ne a baya ya kafa tarihin lashe wasanni 18, wanda ya kafa a kakar wasan 2005-06, karkashin koci Frank Rijkaad.

Madrid wadda ta lashe kofin zakarun Turai da Copa Del Rey a bara, saura wasanni biyar ya rage mata ta doke tarihin lashe wasanni 24 a jere da kulob din Brazil Coritiba ya kafa a shekarar 2011.

Karawar da Madrid za ta yi da Almeria ranar Juma'a, shi ne wasan La Liga na karshe a bana da za ta buga, inda za ta ziyarci Morocco domin buga gasar zakarun kungiyoyin nahiyoyi a mako mai zuwa.