Manchester United ta doke Liverpool da ci 3-0

Man United Liverpool
Image caption United ta bai wa Liverpool tazarar maki 10 tsakani

Kulob din Manchester United ya doke Liverpool da ci 3-0 a gasar Premier wasan mako na 16 da suka kara a Old Traford ranar Lahadi.

Wayne Rooney ne ya fara zura kwallon farko a raga, kafin Juan Mata da Robin van Persie su kara kwallo na biyu da kuma na uku.

Liverpool ta samu damarmakin zura kwallaye a raga musamman ta wajen Raheem Sterling, sai dai golan United David de Gea ne ya hana kwallayen shiga ragar.

Nasarar da United ta samu ya sa tana matsayinta na uku a teburin Premier, ta kuma bai wa Liverpool wadda take mataki na tara tazarar maki 10 tsakani.