CECAFA ta soke gasar wasan bana

Nicholas Musonye
Image caption Habasha ce ta janye daga karbar bakuncin gasar

Gamayyar hukumar kwallon kafar Gabashi da tsakiyar Afirka (cecafa) ta soke gasar cin kofin wasan bana, bayan da ta rasa kasar da za ta dauki bakuncin gasar.

Tun farko an tsara fara gasar tsakanin 24 ga watan Nuwamba zuwa 6 ga watan Disambar bana da kasashe 12, kafin Habasha ta sanar da janyewarta daga karbar bakuncin wasannin.

Sakatare janar na Cecafa, Nicholas Musonye, ya shaida wa BBC cewa sun soke gasar bana, kuma za su tattauna domin fitar da sabbin tsare-tsaren karbar bakuncin gasar.

Cecafa ta ce a shirye take ta rage dawainiyar gasar da nufin rage kudin hidima da zai kara kawata gasar domin jan hankali masoya kwallon kafa a duniya.