UEFA: Man City za ta kara da Barcelona

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Man City za ta fuskanci kalubale a wasanta da Barcelona

Manchester City za ta kece raini da Barcelona a wasan zagaye na biyu a gasar zakarun Turai wanda za a buga a watan Fabarairu.

Chelsea kuwa za ta fafata ne da Paris St-Germain a yayinda Arsenal za ta hadu da Monaco.

Real Madrid za ta kara ne da Schalke sai kuma Atletico Madrid ta kece raini da Bayer Leverkusen.

Bayern Munich za ta raba gari da Shakhtar Donetsk a yayinda Juventus za ta fafata da Borussia Dortmund sai kuma Basel ta hadu da Porto.

Yadda za su hadu:

Za a yi bugun farko a ranakun 17/18/24/25 na Fabarairu

Sai bugu na biyu a ranakun 10/11/17/18 na Maris.

  • Paris St-Germain v Chelsea
  • Manchester City v Barcelona
  • Bayer Leverkusen v Atletico Madrid
  • Juventus v Borussia Dortmund
  • Schalke v Real Madrid
  • Shakhtar Donetsk v Bayern Munich
  • Arsenal v Monaco
  • Basel v Porto