Capital Cup: Chelsea ta kai wasan daf da na karshe

Derby Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea ce ta daya a kan teburin gasar Premier bana

Kulob din Chelsea ya kai wasan daf da na karshe a gasar Capital One Cup, bayan da ya doke Derby County da ci 3-1 a karawar da suka yi ranar Talata.

Eden Hazard ne ya fara zura kwallon farko daga damar da ya samu tun daga tazarar yadi 20, kafin Felipe Luis ya kara ta kwallo ta biyu a raga.

Derby County ta zare kwallo daya ta hannun Craig Bryson, sai dai ta kammala karawar da 'yan wasa 10 a fili, bayan da aka bai wa Jake Buxton jan kati.

Dan wasan Chelsea mai tsaron baya Kurt Zouma sai canja shi aka yi a wasan sakamakon raunin da ya ji a kansa, kuma Andre Schurrle ne ya ciwa Chelsea kwallonta na uku a wasan.