Mu rage dogara da Wilfried Bony — Williams

Wilfred Bony Hakkin mallakar hoto huw evans picture agency
Image caption Bony zai wakilci Ivory Coast a gasar cin kofin nahiyar Afirka

Kyaftin din Swansea Ashley Williams, ya ce ya kamata kulob din ya rage dogaro da Ashley Williams cewar shi ne zai ci musu kwallo.

Dan wasan Ivory Coast, mai shekaru 26, ya zura kwallaye takwas daga cikin wasanni 13 da ya buga a gasar Premier ta bana.

Wasa daya kacal Swansea ta lashe daga cikin wasanni biyar na baya da ta buga, kuma Williams ya yi kira ga 'yan wasansu da su saka kaimi wajen zura kwallaye a raga.

Swansea za ta yi rashin Bony na tsawon lokaci, saboda zai wakilci kasarsa a gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a fara daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairu.

Bony ne ya zura kwallo a raga a karawar da Tottenham ta doke su da ci 2-1 a gasar Premier a wasan mako na 16 da suka kara a filin wasa na Liberty.