Thierry ya yi ritaya daga buga kwallo

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Henry ya lashe kofuna daban-daban

Tsohon dan kwallon Arsenal Thierry Henry ya bayyana cewa ya yi ritaya daga buga kwallon kafa bayan ya shafe shekaru yana cin kofuna daban-daban.

Thierry ya ce yanzu zai zama mai sharhi a fannin wasan kwallon kafa.

Dan wasan, mai shekaru 37 wanda ya lashe gasar cin kofin duniya a shekarar 1998, ya bar kulob din Red Bulls da ke New York a wannan watan, kuma an yi ta jita-jitar cewa zai koma wani kolob din.

Henry ya bayyana cewa tamaular da ya taka abin alfahari ne.

Yanzu haka dai zai koma gidan talabijin na Sky Sports bayan ya yi wa BBC sharhi lokacin gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil.