AFCON: Genoveva ta nemi a dage kofin Afirka

Genoveva Anonma Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tsohuwar gwarzuwar 'yar wasan Equitorial Guinea

Tsohuwar gwarzuwar 'yar wasan kwallon kafar Equitorial Guinea, Genoveva Anonma, ta yi kira da a dauke gasar cin kofin nahiyar Afirka da kasarta za ta karbi bakunci a badi.

'Yar wasan ta yi wannan kiran ne saboda tsoron kada 'yan kasarta su kamu da cutar Ebola.

Equitorial Guninea ce ta maye gurbin Morocco lokacin da kasar ta bukaci hukumar kwalllon kafar Afirka ta dage gasar daga lokacin da ta tsara a gudanar.

Anonma ta ce "ina fargabar na yi hulda da jama'a, ya kamata su soke karbar bakuncin gasar saboda ceton rai da kuma makomar kasarmu".

Kimanin mutane 6,856 ne suka mutu ya zuwa 15 ga watan Disamba, daga kasashe shida da suka hada da Liberia da Guinea da Saliyo da Nigeria da Amurka da kuma Mali.