Kwesi Appiah ya zama kocin SC Khartoum

Kwesi Appiah Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Appiah ne ya jagoranci Ghana a gasar cin kofin duniya da aka kammala a Brazil

Tsohon kocin tawagar kwallon kafar Ghana, Kwesi Appiah, ya karbi aikin horar da kulob din SC Khartoum na tsawaon kwantiragin shekaru biyu.

Kulob din Khartoum zai buga gasar cin kofin zakarun Afirka wato Confederation Cup, bayan da suka kare a mataki na hudu a gasar cin kofin Premier Sudan.

Kocin zai fuskanci kalubale a gasar wasannin Sudan din daga kungiyoyin Al Merreikh da Al Hilal da suka lashe kofin gasar kasar tun daga shekarar 1970, in banda 1992.

Appiah wanda ya jagoranci Ghana a gasar cin kofin duniya da aka kammala a Brazil, sun raba gari a watan Satumba.