Real Madrid ta lashe wasanni 21 a jere

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid za ta buga wasan karshe ranar Asabar

Dan kwallon Wales, Gareth Bale ya zura kwallo daya a wasan da Real Madrid ta doke Cruz Azul ta Mexico da ci hudu da nema a wasan zakarun kungiyoyi na duniya.

Wannan ne nasara ta 21 a wasanni a jere da Real ta samu galaba.

Abin mamaki, dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo wanda ya ci kwallo a wasanni 10 a jere, a wannan karan bai zura kwallo ba.

Real za ta hadu da zakarun kwallon kudancin Amurka, San Lorenzo ko Auckland City a wasan karshe na gasar da ake buga wa Morocco.

Ramos da Benzema da kuma Isco ne sauran 'yan wasan da suka ci kwallo a wasan.