An ci tarar Balotelli an kuma dakatar da shi

Mario Balotelli Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool na fama da kalubale a kakar wasannin bana

Hukumar kwallon kafar Ingila ta ci tarar dan kwallon Liverpool, Mario Balotelli ta kuma dakatar da shi daga buga wasa daya.

Hukumar, wadda ta dakatar da dan kwallon dan Italiya nan take, ta ce ta ci tararsa fam 25,000, sakamakon samunsa da yin kalamun batanci da cin zarafi a shafinsa na sada zumunta.

Haka kuma hukumar ta umarci dan wasan da ya koma makaranta domin ya sami ilmin dabi'u kyawawa.

Balotelli mai shekaru 24 ya amince da hukuncin da hukumar ta yanke masa, kuma ya rubuta mata cewar laifin da ya aikata ba mai girma bane.

Dan wasan ya rubuta cewar "Ka zama kamar Mario; mai gyaran famfo ne dan Italiya, wanda Japanawa suka samar, yana magana da harshen Ingilishi, sannan ya yi kama da dan Mexico."