League One Cup: Chelsea za ta kara da Liverpool

Chelsea Players Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea ce ta daya a kan teburin Premier

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea za ta karbi bakuncin Liverpool a gasar League One Cup wasan daf da na karshe a filin Stamford Bridge.

Kungiyoyin biyu sun kara ranar 8 ga watan Satumba a gasar cin kofin Premier, inda Chelsea ta lashe karawar da ci 2-1.

Tottenham wadda ta yi waje da Newcastle da ci 4-0 ranar Laraba za ta kara da Shieffield United a filin White Hart Lane.

Sheffield United wadda take buga gasar League Cup ta yi waje da kungiyoyin da suke buga Premier da suka hada da Southmpton da West Ham a gasar.

Karawar da za suyi gida da waje, za kuma su fara wasanin ne a cikin watan Janairu, sannan a buga wasan karshe ranar 1 ga watan Maris.