Club World Cup: Madrid za ta kara da San Lorenzo

Real Madrid
Image caption Real Madrid ta buga wasanni 21 a jere ba a doke ta ba

Kulob din Real Madrid zai kara da San Lorenzo a wasan karshe na cin kofin duniya na zakarun kungiyoyin nahiyoyi ranar Asabar a Morocco.

Madrid wadda ta lashe wasanni 21 ba a doke ta ba a wasannin da ta buga, ta kai wasan karshe ne bayan da ta doke Cruz Azul da ci 4-0 ranar Talata.

Kulob din San Lorenzo ya kai wasan karshe ne bayan da ta doke Auckland City da ci 2-1 ranar Alhamis.

Real Madrid na fatan lashe kofin gasar domin ta ci gaba da kafa tarihin tsawaita yawan wasanni ba tare da an doke ta ba.