FIFA za ta fitar da rahoton Micheal Gracia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kuma za a saki rahoton ne da zarar an kammala bincike kan mutane biyar

Manyan jami'an hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA sun amince da yawu daya cewa za a wallafa rahoton binciken da aka yi kan zargin hukumar da karbar na goro, kan daukar bakuncin gasar a shekarar 2018 da 2022.

Hukumar za ta fitar da bangaren rahoton Michael Gracia da take ganin ya dace a wallafa ne a hukumance.

Kawo yanzu dai an wallafa takaitaccen rahoton mai shafuka 430 kan binciken hanyoyin da aka bi wajen amincewa da ba da daukar nauyin gasar kwallon kafar biyu.

Sakin baki daya rahoton, wanda kila an dan saya wasu abubuwa saboda kare wadanda suka ba da shaida, wani sauyin matsayin ne da hukumar ta yi.

Tun da fari FIFA ta ki ba da kai bori ya hau kan matsin lambar da Gracia da wasu mutane suka yi wa hukumar na a wallafa rahoton.

Gracia ya yi zargin rahoton da aka fitar na binciken da ya kwashe shekaru biyu yana yi a cike yake da kura-kurai kuma ba a wallafa shi baki daya ba.