Arsenal za ta ba da aron Sanogo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Murmurewar Olivier Giroud ya takaita damar da Sanogo ke da ita

Kulob din kwallon kafa na Arsenal zai ba da aron dan wasan gabansa Yaya Sanogo a lokacin musayar 'yan wasa a watan Janairu.

Dan wasan dan Faransan mai shekaru 21 ya koma Arsenal ne a lokacin da kwantiraginsa da kulob din Auxerre a shekarar 2013 ya kare.

Sai dai ya ciwo wa kulob din kwallo daya ne tilo a wasanni 19 da ya buga.

Akwai yi wuwar a ba da aron Sanogo ga wani kulob din da ke cikin premier league maimakon wata kasa ta ketare.