Van Gaal bai ji dadin yin kunnen doki da Villa ba

Louis van Gaal Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Har yanzu United tana matsayi na 3 a teburin Premier

Kocin Manchester United Louis van Gaal ya ce bai kamata su tashi wasa kunnen doki da Aston Villa ba, idan har suna son lashe kofin bana.

Aston Villa ce ta fara zura wa United kwallo kafin Falcao ya farke mata a karawar da suka yi a gasar Premier ranar Asabar a Villa Park.

Hakan yasa United tana matsayinta na uku a teburin Premier, kuma Chelsea wadda take mataki na daya ta ba ta tazarar maki bakwai kafin ta kara da Stoke City ranar Litinin.

Van Gaal ya ce "Idan har kana son lashe kofin bana, to ya kamata ka doke kungiya kamar Aston Villa".

Bayan da aka tashi wasan kyaftin din United, Wayne Rooney, ya ce 'yan jaridu ne suke saka United cikin wadan da za su iya lashe kofin Premier bana.