An ribanya kyautar lashe kofin duniya na mata

women-worldcup Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Japan ce mai rike da kofin duniya na Mata da ta dauka a 2011

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta ninka kudin lashe kofin duniya na mata da za a buga a shekarar badi da Canada za ta karbi bakunci.

Duk kasar data lashe kofin badi za a bata dalar Amurka miliyan biyu, wanda a shekarar 2011 dalar Amurka miliyan daya aka bai wa Japan wadda ta dauki kofin.

FIFA za ta rabawa kasashen da suka halarci gasar da Canada za ta karbi bukunci kudi da zai kai dalar Amurka miliyan 15, wanda shekaru hudu baya dala amurka miliyan 10 ta raba.

A gasar cin kofin duniya da aka kammala a Brazil dalar Amurka milyan 576 FIFA ta bai wa kasashen da suka halarci gasar, yayin da Jamus wadda ta lashe kofin aka bata dalar Amurka miliyan 35.