Real Madrid ta lashe kofuna hudu a bana

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid ce ta daya a kan teburin La-Liga Spaniya

Kungiyar Real Madrid ta lashe kofuna hudu a bana, bayan da ta doke San Lorenzo, a gasar cin kofin duniya na zakarun kungiyoyin nahiyoyi da suka kara ranar Asabar a Morocco.

Madrid ta fara zura kwallon farko ne ta hannun Sergio Ramos, kafin Gareth Bale ya kara kwallo na biyu a raga.

Nasarar da Madrid ta samu yasa ta dauki kofi na hudu kenan a bana, wanda tun farko ta lashe kofin zakarun Turai da Copa del Rey da Super Cup na Turai.

Haka kuma kungiyar ta tsawaita yawan lashe wasanni 22 a jere ba a doke ta ba a bana.

Wannan ne karon farko da Madrid ta lashe wannan kofin, sai dai ta taba daukar Intercontinental Cup a shekarar 1960 da 1998 da kuma 2002.