Hukumar kwallon kafar Saliyo ta shiga rikici

Isha Johansen
Image caption Hukumar FIFA, har yanzu ba ta ce komai ba dangane da rikicin

Mambobin hukumar kwallon kafar Saliyo SLFA, sun rushe kwamitin amintattun hukumar kwallon kafar kasar karkashin shugabancin madam Isha Johansen.

Tuni suka maye gurbinta da Alhaji Unisa Alim Sesay a matsayin shugaba tare da mambobi takwas da za su jagoranci hukumar zuwa watan Yunin 2015 lokacin da za a yi sabon zabe.

Hukuncin da suka dauka daya ne daga cikin hukunce-hukunce tara da mambobin hukumar 12 daga cikin 14 da suka zartar a wani salon taro da ba a saba yin irinsa ba.

An gudanar da taron ne ta wayar sadarwa, kasancewar an rufe harabar hukumar, sakamakon hutun da aka bayar a kasar domin rage yaduwar cutar Ebola.

Sai dai Johansen bata amince da hukuncin da mambobin hukumar kwallon kafar su zartar ba, har ma ta soki taron nasu da cewa haramtacce ne.