An cire wa 'yan kallon kwallon Masar takunkumi

Eqypt Fans Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masar ta yi fama da tashin kankali a filayen wasa karo da dama

An dage takunkumin da aka sakawa magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa na hana su shiga filin wasa a shekaru uku da suka wuce.

Tun lokacin da aka samu yamutsi a filin wasa na Port Said da ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan kallo 70 aka hana magoya bayan kungiyoyin shiga kallon wasa.

Hukumar kwallon kafar Masar ta sanar da cewa ministan cikin giga ne ya amince da a bar magoya baya su dinga shiga filin wasa, lokacin da za a koma zagaye na biyu na gasar kasar.

Hukumar ta ce 'yan kallo 10,000 za a bari su shiga filin wasanni a Alkahira da sannan magoya baya 5,000 ne za su kalli wasa a sauran filayen da ke biranen kasar.