Charlie Austin ba zai bar QPR ba — Redknapp

Charlie Austin
Image caption QPR tana mataki na 16 a teburin Premier da maki 17

Kocin Queens Park Rangers, Harry Redknapp, ya ce ba zai bari wani kulob ya daukar masa dan wasansa Charlie Austin ba a watan Janairu.

Austin, mai shekaru 25, ya kuma zura kwallaye 11 a gasar Premier, har da kwallaye ukun da ya ci West Bromwich a karawar da QPR ta doke su 3-2 a gasar Premier ranar Asabar.

Redknapp ya ce suna bukatar dan kwallon domin ya ci gaba da ciwo musu kwallaye, kuma yana sa ran zai zura kwallaye 20 a gasar Premier bana.

Kwallaye 17 QPR ta ci a filin wasanta na Loftus Road, inda Charlie Austin ya ci kwallaye tara.

Austin ya koma QPR ne daga Burnley a farkon kakar wasan bara, kuma saura watanni 18 kwantiraginsa ya kare da kulob din.