An gina mutum-mutumin Ronaldo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mahaifiyarsa ta ce Ronaldo ba zai taba mantawa da asalinsa ba.

Dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya je garinsu Funchal da ke tsibirin Madeira inda ya bude mutum-mutuminsa da aka ginamai tsawon mita 3.4.

Dan wasan, mai shekaru 29 a duniya ya ce, "wannan lokaci ne na musamman a gare ni, kasancewa an gina mutum-mutumina a wannan garin."

Mutum-mutumin dai yana daga cikin abubuwan tarihi wadanda yake adanawa domin tunawa da rayuwarsa ta kwallon kafa.

Cikin abubuwan da ya ajiye a "gidan tarihinsa" akwai kyatukan da ya lashe na kasance gwarzon dan kwallon kafar duniya a shekarar 2008 da 2013.

Ronaldo dai ya zura kwallaye 34 a wasanni 27 da ya buga a kakar wasanni ta bana kawai.

Mafaifiyarsa Dolores Aveir ta ce, "Ronaldo bai taba mantawa da asalinsa ba".