An janye jan katin da aka bai wa Agbonlahor

Gabriel Agbonlahor Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan zai buga karawar da za su yi da Swansea City kenan

An janye jan katin da aka bai wa Gabriel Agbonlahor dan wasan Aston Villa a karawar da suka yi da Manchester United, bayan da aka shigar da korafi.

An bai wa Agbonlahor jan kati ne bayan an dawo daga hutu a lokacin da ya yi wa tsohon dan kwallon Villa Ashley Young keta.

Sakamakon wannan hukuncin da aka yanke, dan kwallon zai buga a fafatawar da za su yi da Swansea City ranar Juma'a.

Sai dai an tuhumi kulob din da kasa tsawatar wa 'yan wasansa a lokacin da aka bayar da jan katin, inda suka ta da yamutsi.

An kuma bai wa Aston Villa daga nan zuwa 30 ga watan Disamba domin ya kare kansa daga tuhumar da aka yi masa.