Yedlin zai koma Tottenham a Janairu

De Andrea Yedlin Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tottenham tana matsayi na bakwai a teburin Premier

Kulob din Tottenham ya sanar da cewar dan kwallon Seattle Sounders, De Andre Yedlin, zai koma buga musu tamaula daga watan Janairun badi.

Dan wasan Amurka, mai shekaru 21, ya rattaba kwantiragin buga wa Tottenham kwallo tun a watan Agusta, kuma sai yanzu ne ya sami izinin taka leda a Ingila.

Kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya ce yana fatan dan wasan zai yi saurin sabawa da yanayin kasar da salon buga wasannin kulob din.

Yedlin ya buga wa tawagar kwallon kafar Amurka wasanni 10, ya kuma buga gasar cin kofin duniya karo uku a canji dan wasa.