Watakila Torres ya koma Atletico Madrid

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Torres na shan suka a San Siro

Dan kwallon Chelsea, Fernando Torres zai iya koma wa tsohuwar kungiyarsa Atletico Madrid ta Spain.

Dan kwallon Spain din wanda ya koma AC Milan a matsayin aro na shekaru biyu daga Chelsea a watan Agusta, har yanzu bai zura kwallo ba a San Siro.

Shugaban Atletico, Enrique Cerezo ya nuna alamun watakila angulu ta koma gidanta na tsamiya.

A shekara ta 2007 ne Torres ya bar Atletico Madrid ya koma Liverpool.