Man Utd za ta dauki kambun Premier-Van Gaal

Hakkin mallakar hoto
Image caption Van Gaal

Manajan Kulob din Manchester United, Louis Van Gaal, ya ce burin da suka sa a gaba shi ne na ganin kulob din ya lashe kofin gasar Premier League.

"Har yanzu burinmu shi ne kulob dinmu ya zamo zakara a karshen kakar wasan Premier League. Ko yaushe mu kasance na farko", In ji Van Gaal.

Kulob din Manchester City dai ya lallasa Man Utd a farkon watan Nuwamba da ci 1-0, abin da ya sa kulob din da Van Gaal ke jagorantar ya fara kakar wasannin da kafar hagu, wanda rabon kulob din ya ga haka tun a shekarun 1986 zuwa 87.

Sai dai kuma kociyan mai shekaru 63 ya nanata cewa kulob din nasa ya fara farfadowa ne, kuma hakan zai iya daukar tsawon shekaru uku.

A yanzu haka Man Utd ta na biye wa kulob din Chelsea da maki 10.