Torres zai koma AC Milan dindindin

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Torres ya taimaka wa Chelsea lashe kofin zakarun Turai da kofin kalubale.

Kungiyar AC Milan ta dauki tsohon dan kwallon Chelsea Fernando Torres domin ya koma buga mata wasa na dindindin daga ranar 5 ga watan Janairu.

Torres, mai shekaru 30, ya koma AC Milan a watan Agusta aro kan yarjejeniyar kwantiragin shekaru biyu.

BBC ta fahimci cewar AC Milan za ta bayar da Torres aro zuwa Atletico Madrid a watan gobe, a inda za a yi mata musaya da dan kwallon Italiya Alessio Cerci.

Torres ya koma Chelsea ne daga Liverpool a matsayin dan wasan da aka saya mafi tsada kan kudi fam miliyan 50 a watan Janairun 2011.