An bai wa Pardew damar ganawa da Crystal Palace

Image caption Crystal Palace tana matsayi na 18 a gasar Premier

Kulob din Newcastle ya bai wa Alan Pardew izinin fara tattauna wa da Crystal Palace domin ganin ko zai iya komawa can.

Kungiyoyin biyu sun cimma yarjejeniya yadda za a biya Pardew ladansa na barin St James Park, domin maye gurbin Neil Warnock wanda aka sallama.

Tuni ma Newcastle ta sanar da cewa Pardew ba zai jagoranci atisayen kulob din ranar Talata ba.

Ta maye gurbinsa da mataimakinsa John Carver a matsayin kocin rikon kwarya.

Crystal Palace tana matsayi na 18 a teburin Premier da maki 16, kuma wasanni uku kacal ta lashe a gasar wasannin bana.