Newcastle ta nada kociyan rikon-kwarya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An nada sabon kociya a Newcastle

Newcastle United ta sanar da sunan Alan Carver da Steve Stone a matsayin wadanda za su jagoranci kulob din a wasanni biyu na gasar Premier.

Kulob din ya dauki wannan matakin ne domin maye gurbin Alan Pardew wanda yake tattaunawa da Crystal Palace a matsayin sabon kociyanta.

Tuni kulob din ya sanar da cewar Pardew ba shi ne zai jagoranci atisayen ‘yan was a ranar Talata ba, inda Carver da Stone ne za su fara aikinsu.

Za kuma su jagoranci Newcastle buga gasar Premier da za su fafata da Burnley ranar Alhamis da kuma kofin kalubale da za su buga da Leicester ranar Asabar.