Real Madrid za ta fafata da AC Milan

Image caption A kakar wasan bana Madrid ta buga wasanni 28, a inda ta lashe karawa 24 ta yi canjaras a wasa daya aka doke ta wasanni uku.

Real Madrid za ta buga wasan karshe a bana da AC Milan ta Italiya a wasan Dubai International Football Challange ranar Talata.

Madrid dai ta dauki kofuna hudu a bana, cikinsu har da kofin Zakarun Turai da Copa del Rey da Super Cup na Turai da kuma kofin Zakarun nahiyoyin duniya.

Tun daga watan Satumba da Real Madrid ta lallasa Basel da ci 5-1 a gasar cin kofin Zakarun Turai, ta buga wasanni 22 a jere ba a doke ta ba.

Saura wasanni uku Madrid, mai rike da kofin zakarun Turai, ta goge tarihin da kulob din Brazil Coritiba FC ya kafa a shekarar 2011, inda ya lashe wasanni 24 a jere.

A kakar wasan bana Madrid ta buga wasanni 28, a inda ta lashe karawa 24 ta yi canjaras a wasa daya aka doke ta wasanni uku.