Tim Howard zai yi jinyar makwonni shida

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A wasan da suka yi na karshe, sai da aka sauya Howard saboda raunin

Golan Everton, Tim Howard, zai yi jinyar makwonni shida sakamamakon rauni da ya ji a gwiwar kafarsa.

Ko da a fafatawar suka yi da Stoke City a gasar Premier ranar Juma'a sai sauya dan wasan aka yi.

Tuni Joel Robles ya maye gurbinsa, kuma shi ne ya kama wasan da Newcastle ta doke su 3-2 a wasan Premier ranar Lahadi.

Everton tana mataki na 12 a teburin Premier bayan buga wasanni 19, za kuma ta ziyarci Hull City ranar Alhamis 1 ga watan Janairu.